Tinubu Ya Yi Wa Arewa Gata – Martanin Bello Matawalle Ga Dattawan Arewa

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce makaho ne kaɗai zai iya cewa Bola Ahmed Tinubu ya gaza a mulkin da ya fara.

Matawalle ya caccaki ƙungiyar Dattawan Arewa NEF a Karkashin Jagoran Profesor Ango Abdullahi kan barazanar da ta yi cewa Arewa za ta sauya shugaba Tinubu a 2027

Tsohon gwamnan ya ce Tinubu ya shirya yi wa Arewa ayyuka masu yawa kuma NEF ba ta da ikon yanke hukuncin wanda ƴan Arewa za su zaɓa

Duk wanda ke kallon Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko mai rauni, ko dai makaho ne ko ɓataccen da ya kasa ganin sabuwar Najeriyar da ta kunno kai.

Kungiyar dattawan Arewa ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman ta nuna nadamar yadda yankin ya zabi Tinubu a 2023.

Kungiyar ta ƙara da cewa daga yanzu, Arewa za ta fi maida hankali kan haɗa kai wuri ɗaya da maslaha wajen zaɓen ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Amma tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana ƙungiyar a matsayin “nauyin siyasa”, inda ya dage cewa NEF ba ita ba ce, kuma ba za ta taba zama mai magana da yawun Arewa ba. Matawalle ya ce shi da sauran su sune manyan jagororin Arewa ba za su tsaya su zuba ido wasu ‘tsirarun mutane’ sun ɓata wa yankin Arewa suna ba.

“Duk wanda ke kallon Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko mai rauni, ko dai makaho ne ko ɓataccen da ya kasa ganin sabuwar Najeriyar da ta kunno kai”.

Matawalle ya ce duk mai hankali ya ga ayyukan da Tinubu ya ɗauko yi a Najeriya

Neman suna kawai ƙungiyar dattawan Arewa (NEF) ke yi – Amman Gaskiyar magana Shugaba Tinubu na son yankin Arewa kamar ransa -inji ƙaramin ministan tsaro bello Matawalle

Labarai Makamanta

Leave a Reply