Iran ta ?addamar da hare-hare a Isra’ila ranar Asabar da tsakar dare, inda ta harba jirage marasa matu?a da makamai masu linzami fiye da 200.
Iran ta kai wa?annan hare-haren ramuwar gayya ne bayan Isra’ila ta kai hari a ofishin jakadancinta da ke Syria, inda ta kashe zaratan sojinta bakwai ciki har da masu mu?amin janar.
Jirage marasa matu?a da makamai masu linzamin da Iran ta harba shi ne karon farko da take kai hari Isra’ila kai-tsaye daga cikin ?asarta.
Wa?annan hare-hare sun jawo fargaba game da yiwuwar ramuwa daga Isra’ila kan Iran lamarin da zai ?ara zaman ?ar-?ar ?in da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.