Za Mu Inganta Manyan Asibitocin Jihar Kaduna 32 Bayan Watsi Da Gwamnatocin Baya Suka Yi – Uba Sani

IMG 20240310 WA0186

Gwamnan Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa a tsawon shekaru 20 ba a gyara manyan asibitocin Kaduna guda 32 ba, lamarin da ya sa ‘yan jihar ke garzaya wasu jihohi dake makwabtaka da jihar domin neman magani

Gwamna Sani ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga kananan hukumomin jihar 23 da suka kai masa ziyarar barka da Sallah a gidan gwamnati da ke Kaduna.

Bayan haka gwamnan ya ce akalla makarantu sama da 1500 ba a katange su ba wanda suke haɗarin barazanar ƴan bindiga a koda yaushe.

Sai dai ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar gyarawa, sake ginawa da kuma samar da kuma saka kayan aiki a asibitoci guda shida, guda biyu a kowace shiyya a fadin jihar.

Ya ce za a fara gyara a sibitocin dake Gwantu, Rigasa, Maigana, Ikara, Kafanchan da Giwa.

Kuma tun daga ranar Litinin ne aiki zai kankama.

” Mataimakiyar gwamna Hadiza Balarabe waxce fitacciyar malamar asibiti ce ta gudanar da bincike kan asibitocin jihar kuma aka gano cewa dukkan su suna jan gindi ne, babu muhimmin gyara da aka yi musu tun shekaru ashirin da suka wuce”

Daga nan sai gwamnan ya yi albishir cewa wasu attajirai biyu mazauna garin Kaduna, Adamu Attah, da Bukar Shettima sun yi alƙawarin gina katanga kyauta ga makarantu 100 a fadin jihar.

” Ni da kai na na tuntuɓi waɗannan attajirai, kuma suka yi mana alƙawarin katange makarantu 100 kyauta a faɗin jihar daga aljihun su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply