Tallafin Fetur Ba Zai Tabbata Ba – Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sake nanata aniyarsa ta janye tallafin man fetur a 2023, yana mai cewa “ba abu ne mai ɗorewa ba idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa”.

Buhari ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da kasafin kuɗin 2023 na naira tiriliyan 20.51 ga gamayyar taron ‘yan majalisar tarayya a ranar Juma’a.

A cewarsa: “Maganar tallafin mai abu ne mai cike da cecekuce a ƙasarmu tun daga shekaraun 1980.

“Sai dai, halin da ake ciki a yanzu ya nuna cewa ba abu ne mai ɗorewa ba. A matsayinmu na ƙasa, dole ne mu tunkari batun nan da tunanin cewa akwai buƙatar mu samar da tsarin kula da sauran ɓangarori na al’umma.”

Buhari ya ce dakatar da biyan tallafin ya zama wajibi don samun kuɗin gudanar da sauran ayyuka sakamakon ƙarancin kuɗin shiga.

“Yayin da muke neman faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shigarmu, dole ne mu mayar da hankali kan yadda za mu alkinta arzikinmu.”

Wannan ne kasafi na ƙarshe da gwamnatin Buhari ta gabatar yayin da yake shirin sauka daga mulki a watan Mayun 2023, wanda a lokacin ne gwamnatin ke son daina biyan tallafin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply