Saura Ƙiris Da Na Yi Wuf Da Tsohon Shugaban Kasa Babangida – Zee-Zee

Ummi Ibrahim, fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Ummi Zee Zee, ta tabbatar da rade-radin da ke cewa ta yi soyayya da tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja, Ibrahim Babangida (IBB).

Babangida ya mulki Najeriya tsakanin 1985 da 1993. Akwai rahotanni a shafukan sada zumunta da ke cewa jarumar tana soyayya da tsohon Shugaban Kasar.

“IBB saurayina ne amma yanzu bama tare domin na rabu da shi, in ji Ummi Zee Zee. A cikin zantawa da Mujallar Daily Trust ta karshen mako, Zee Zee ta ce lallai ta rabu da IBB.

“Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida saurayina a baya amma ba yanzu ba. “Duk da haka, a yanzu muna abota kuma muna mutunta juna.

A yanzu haka, ina da wani saurayi wanda baya masana’antar nishadantarwa kuma muna shirin yin aure insha Allah. ”

Tsohon shugaban kasar ya rasa Maryam, matarsa a shekarar 2009 kuma bai sake yin aure ba tun lokacin.

Har yanzu kungiyar watsa labarai ta IBB ba ta mayar da martani ba game da ikirarin Zee Zee na yin soyayya da dattijo Shugaban kasar ba.

A wani labarin, duk da jita-jitar mutuwar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), majiyoyi sun ce tsohon shugaban na nan da ransa kuma yana cikin koshin lafiya.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa IBB ya ci gaba da tarbar manyan ‘yan kasa na nesa da na kusa a matsayin maziyartan bikin Eid-el-Fitr a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu, a gidansa na Uphill a Minna, babban birnin jihar Neja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply