Safarar Muggan Kwayoyi: NDLEA Ta Kama Ma’aikatan Tashar Jiragen Ruwa

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce tana tsare da ma’aikata 12 na tashar jirgin ruwan Apapa, dake Jihar Legas saboda yadda suke da alaka da shigo da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 32.9 wanda darajarsa ta kai Naira biliyan 9.5.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, Wanda ya bayyana hakan ranar Asabar yace a ranar 13 ga watan Oktoba ne hukumar ta kama wata jirgi a tashar jirgin ruwa ta Apapa sakamakon bayanan sirri da aka samu daga abokan huldar kasa da kasa da kuma goyon bayan wasu jami’an tsaro irinsu sojojin ruwan Najeriya, kwastam, DSS da kuma ‘yan sanda.

“Binciken da aka yi wa jirgin ya kai ga gano buhunna 30 dauke da hodar iblis, masu nauyin kilogiram 32.9”, in ji Femi Babafemi.

Kakakin ya kara da cewa daga bisani ne Hukumar ta garzaya wata babbar kotun Tarayya dake Legas inda ta samu umurnin tsare matukin Jirgin, Mista Tanahan Krilerk da sauran ma’aikatan jirgin ‘yan Kasar waje su 21.

Labarai Makamanta

Leave a Reply