Jahilci Ne Ke Haddasa Auren Wuri – Sunusi

Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce rashin inganta tsarin ilimi ne ke janyo auren wuri a arewacin Najeriya.

Wata tattaunawa da aka yi da tsohon sarkin ta kafar Zoom ya ce idan har ana son magance matsalar auren wuri dole sai an inganta tsarin ilimi da samar da makarantu da kuma tilasta ilmi ga ‘ya’ya mata.

Tsohon sarkin ya soki gwamnatoci inda ya ce ba za su iya magance matsalar auren wuri ba saboda ba su samar da makarantu da tsarin ingantaccen ilimi.

Ya ce akwai dokar hukumar ilimin bai-daya ta UBE da ta haramta aurar da yarinyar da ba ta kammala aji uku na sakandare ba, kuma a cewarsa dokar ta shafi har da hukunta malaman da suka daura auren.

“Amma babu wanda aka hukunta domin wanda ya kamata ya kai karar iyayen ba zai iya ba saboda bai samar da makarantun ba.” inji shi.

Tsohon sarkin na Kano ya ce muhawara ce ya kamata a yi – “Mu tambayi kanm u kan shekarun da ya dace a aurar da ‘ya mace”

“Na zama sarki tare da sanin yadda tunanin mutanenmu na arewa yake yadda suke son aurar da ‘yayansu.”

“Kuma kasancewa ta sarki wanda ya fahimci gaskiyar yanayin talakawa, suna son ilmantar da ‘ya’yansu amma babu makarantun.

A cewarsa wani lokaci uba zai tura ‘yarsa makarantar firamare amma zai kasance ba tare da ta koyi komi ba, don haka sai ya ga babu wani riba a ilimin.

“Ya kamata a ce sai yarinya ta kammala karatun sakandare kafin a yi mata aure.” inji Sarki Sanusi.

Da alama dai wannan matsalar ta damu Sarki Sanusi II domin ya sha fitowa fili yana tsokaci kan batun da ya shafi auren wuri da ilimin ‘ya’ya mata.

A lokacin da yana kan karagar sarautar Kano, sarki Sanusi II ya taba ya bayyana adawarsa kan yadda ake yawan auren mace fiye da daya ana suna haihuwar ‘ya’ya da dama ba.
Madogara: BBC Hausa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply