Najeriya Za Ta Sake Afkawa Cikin Kwazazzabon Talauci – Masana

IMG 20240225 WA0030

Shugaban Cocin INRI Evangelical Church, Primate Ayodele ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya canza salonsa na farfado da tabarbarewar tattalin arziki saboda har yanzu akwai tarin matsalolin a fannin tattalin arziki a Nijeriya.

An ruwaito cewa, Ayodele ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu

Ya bayyana cewa har yanzu abubuwa za su ci gaba da tsada kuma za a kara samun hauhawar farashin kayayyaki matukar gwamnati ba ta inganta harkar noma da tabbatar da samar da man fetur mai sauki da kuma ci gaba da samar da wuraren da za rika tace man fetur a kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply