Duniyar Fina-Finai: Jarumi Ahmad Tage Ya Kwanta Dama

Ƴan wasan fina-finan Kannywood na alhinin rasuwar abokin sana’arsu Ahmad Tage wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

Ahmad Tage ya rasu ne bayan jinyar rashin lafiya a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano.

Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro.

‘Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 21.

Tuni ‘yan wasan Hausa na Kannywood suka shiga alhini tare da mika ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya sanar da labarin mutuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram tare da yi masa rokon gafarar Allah.

Taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood da dama ne suka bayyana alhinin rasuwar Ahmad Tage.

Taurari irin su Saratu Daso da Maryam Booth da Abdullahi Nuhu da mawaƙa irin su Ado Gwanja sun yi wa mamacin addu’ar Allah ya jikansa.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Jaruma Saratu Daso ta ce mamacin wanda darakta ne kuma Jarumin kuma mai ɗaukar hoto ya rasu ne a ranar Litinin.

Daso ta yi masa addu’ar rahamar Allah.

Shahararren mawakin zamani kuma jarumin fina-finan Kannywood Ado Gwanja shi ma ya aika da ta’aziyyarsa a shafin na Instagram.

Ya ce: “Allah ya jaddada rahama a gareka mutumin kirki Allah ya sa ka huta.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply