Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincikar El-Rufa’i

IMG 20230808 WA0052(1)

Majalisar dokokin Kaduna ta kaddamar da binciken basukan da El-Rufai ya ciwo, kwangiloli, da kuma bankado harkallar da ake zargin gwamnatin ta tafka

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki kudaden da gwamnati tsohon gwamna Nasir El-Rufai ta kashe, basukan da aka ciwo, Lamuni da tallafin da gwamnatin ta samu kwangilolin da ka bada, su wa aka ba, wadanda ka kammala, wadanda ba a kammala ba, da dai sauransu.

Hakan ya biyo bayan korafi ne da Gwamna Uba Sani ya yi a wurin taron masu ruwa da tsaki na jihar Kaduna, inda ya koka da wasu basussuka da suka kai dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangiloli har na Naira biliyan 115 da gwamnatocin baya suka bari.

Kwamitin majalisar za ta gayyaci duk wani jigo a gwamnatin El-Rufai da suka hada da kwamishinonin sa, tsohon kakakin majalisa, hadiman sa na kusa, da kuma shugabannin ma’aikatun gwamnati da sauransu.

Bayan tattaunawa, shugaban majalisar ya bayyana cewa kwamitin wucin gadi zai binciki ayyukan da aka yi watsi da su da kuma basussukan kasashen waje da gwamnatin da ta gabata ta karba, domin mazauna jihar na da hakkin a sanar da su halin da jihar ke ciki.

Mambobin kwamitin wucin gadi sun hada da Hon Lawal Aminu mai wakiltar mazabar Doka/Gabasawa a matsayin shugaba. Sauran mambobin sun hada da Hon Mugu Yusuf, mai wakiltar mazabar Kaura; Shugaban masu rinjaye Munira Sulaiman Tanimu; da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Shehu Yunusa Pambegua, da dai sauransu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply