Matsalar Tsaro: Za Mu Dawo Da Tsoffin Soji Bakin Daga – Shugaban Dakarun Soji

Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa za ta dawo da tsoffin sojojin da su ka yi ritaya domin su shiga ayyukan dakile barazanar matsalar tsaro a kasar nan.

Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ne ya bayyana haka, a ranar Talata, kokacin da ya ke jawabi a wani taron sanin makamar aiki na farko na 2021, da aka shirya wa tsoffin sojoji a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Sunan taron dai “Hanyoyin Amfani da Basirar Tsoffin Sojoji Domin Samar Da Tsaro a Kasa.”

Attahiru wanda Shugaban Bangaren Kula da Ayyukan Ma’aikata na Sojojin Najeriya, Manjo Janar Abdulrasheed Aliyu ya wakilta, ya ce har yanzu tsoffin sojoji na da rawar da za su taka, duk da cewa sun yi ritaya daga aikin soja.

“Mun yanke shawarar daukar su domin taya sojoji ayyukan dakile matsalolin tsaro, ganin cewa kalubalen da kasasr nan ke fuskanta ya mamaye yankuna da dama a kasar nan. Kuma a batun dakile matsalar tsaro, ai kowa ma na da rawar da zai iya takawa domin samar da tsaro a kasar nan.

“Don haka su ma tsoffin sojojin da su ka yi ritaya da wadanda aka sallama daga aiki, su na da rawar da za su iya takawa, musamman a wannan mawuyacin lokacin da aka shiga, wanda kasar nan ke fuskantar matsalar rashin tsaro.

“Saboda haka an shirya wannan taron sanin makamar aiki domin a shirya kuma a karfafa wadanda za su shiga wannan aiki mai muhimmanci wajen dakile matsalolin tsaro da hana aikata mugga da kananan laifuka.” Inji Attahiru.

“Wannan taro zai yi kokarin fadada kwarewa da fasahar ilmin dakile matsalar tsaro da tsoffin sojojin ke da ita, domin a karfafa samar da tsaro a kasar nan.”

Attahiru ya ce an shirya wannan gagarimin aiki domin a dakile duk wata matsalar tsaron da ke damun kasar nan a cikin gida da kuma wadda ake fuskanta daga wajen kasar nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply