Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bawa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa gwamnatin ba za ta yi watsi da gajiyayyu da talakawa ba, za ta cigaba da tallafa musu kamar yadda ta fara.
Shugaban kasa ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da hadimisa kan watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ranar Alhamis a yayin da kirista ke shirin bikin Easter, kamar yadda jaridar Channels Tv ta ruwaito.
Ya ce. “A matsayin mu na gwamnati, za mu cigaba da tabbatarwa ba mu manta da gajiyayyu, talakawa da marasa galihu a cikin mu ba.
“Mun taimaka musu da tallafi duk da cewa akwai karancin kudi, mun yi iya kokarin mu wurin taimakawa iyalai da masu sana’o’i da abin ya shafa a wannan lokacin.