Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Najeriya – Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta na barazanar gurgunta shirin aike jami’an tsaro da albarkatun kasa da kuma yanayin tsaro a faɗin kasar.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da wani daftari na takaita rikice-rikice ta kasa da nufin cike giɓin da aka samu ta hanyar aike jami’an tsaro masu yawa ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Shirin da ofishin mai ba shugaban shawara kan harkar tsaro da kuma hadin gwuiwa da hukumomi, zai tabbatar da cewa an samu nasara wajen dakile rikice-rikice a fadin kasar.

Buhari ya tuna cewa a lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, Najeriya na fuskantar matsalolin rashin tsaro da dama kama daga ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da satar danyen mai da sauransu.

Har ila yau, shugaba Buhari ya jinjinawa mai taimaka masa a bangaren sha’anin tsaro da kuma sauran hukumomi saboda samar da shirin, inda ya ce hakan ya nuna zimmar da ake da ita na ganin an magance rikice-rikce a fadin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply