Masu Zargin Uba Sani Kan Bashin El-Rufa’i Sun Jahilci Aikin Majalisa – Barista Ibrahim Bello

IMG 20240421 WA0094~2

An bayyana cewa dukkanin jama’a da ke zargin Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani da cewa da goyon bayansa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ciyo bashin da ake bin jihar, sun jahilci aikin majalisa.

Mataimaki na musamman ga Gwamna Uba Sani kan harkokin Masarautu Honorabul Barista Ibrahim Bello Rigachikum ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Barista Ibrahim Bello wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne mai wakiltar karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ya ƙara da cewar alfarma ce Uba Sani ya nema a lokacin yana Sanata a gaban majalisa domin ganin an samu bashin saboda kyautata zato da yake dashi na za a aiwatar da ayyukan ciyar da jihar Kaduna gaba, bai ga wadannan kudi ba, ba ta hannun sa suka shigo ba.

Dangane da ayyukan raya jiha da gwamna Uba Sani ke yi a Jihar Kaduna kuwa, Barista Ibrahim Bello ya ce a tarihin jihar ba a taɓa samun jajirtaccen gwamna kamar Sanata Uba Sani ba, duk da kalubale da ya fuskanta a farkon hawa kujerar mulki na ƙiƙi-ƙaƙar shari’ar zaɓe bai hana shi aiwatar da ayyukan ciyar da jama’ar Jihar Kaduna gaba ba.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan ya yi kira ga kafatanin jama’ar Jihar Kaduna da su goya wa Gwamna Malam Uba Sani baya a kokarin da yake na dawo da martabar jihar Kaduna da inganta rayuwar al’ummarta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply