Kwashe Almajirai: Za Mu Yi Maganin Ka Da Qur’ani – Bauchi Ga El Rufa’i

Sheikh Nazir Ɗahiru Usman Bauchi ɗaya ne daga cikin ‘ya’yan Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya bayyana a cikin wani faifan Bidiyo yana mayar da martani mai zafi ga El Rufa’i sakamakon kwashe musu Almajirai da ya yi da sunan kariya daga CORONA.

Sheikh Nazir Ɗahiru Bauchi ya bayyana cewar Gwamnan Kaduna El Rufa’i yayi kuskure daya tura jami’an tsaro cikin dare suka je suka afka cikin gidan mutane bayin Allah na barci aka harba masu tiyagas batare da wata takarda umarni (warrant) data basu iznin shiga gidan ba, wanda dole a doka sai da ita.

Sannan ya bayyana cewar kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba kowane ɗan kasa ciki harda Almajirai iznin zama aduk inda suke so ba kuma wanda ya isa ya hanasu wannan ‘yancin nasu.

Nazir Ɗahiru Bauchi ya ƙara da cewar tabbas kowanne Almajiri zai iya zama garinsa yayi karatu ba tare da yaje wani guri ko yawon bara ba, to amma su shugabannin sune suka taka muhimmiyar rawa wajen gadarwa da ‘yan kasa talauci inda suke kai ‘ya’yan makarantun kasashen duniya daban daban, amma sun bar ‘ya’yan talakawa cikin ƙunci da talauci.

Malamin Ɗarikar ya kuma ƙalubalanci gwamnan kan yadda shima ya tara dukiyarsa tare da cewa halattattu da haramtattun hanyoyi mafi yawanci akabi tare da tuhumar sana’ar gwamnan kan sana’arsa tare da cewa su Almajirai an watsar dasu duk da suna da ‘yanci amma basu taba yin wata zanga-zanga ba, sun hakura sun rungumi Qur’ani babu ruwansu da duk wani surkullenku amma kun tsanesu kun taso su gaba kuna neman ganin bayan su.

“Idan gyara kuke son kawowa ba rushe tsarin karatun Qur’anin ba da nemo ahlin sa zaku yi amma yanzu ta bayyana rushe tsarin kawai kukeson yi”.

Don haka ba zamu yarda ba zamu bi duk tsarin da doka ta bamu wajen kwatar masu hakkinsu sannan a sani Wallahi karshen duk wani mai wulakanta Qur’ani da makarantansa bazai yi kyau ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply