Izala Ta Goyi Bayan Zaman Mukabala Tsakanin Abdul-Jabbar Da Malaman Kano

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa I?amatus Sunnah ta Kasa ta fito fili inda ta bayyana goyon baya dangane da matakan da gwamnatin Kano ta ?auka na da?ile fitinar da Abdul-Jabbar ke haddasawa tare da yaba zaman mu?abala da aka shirya tsakanin shi da Malaman Kano.

Shugaban Kungiyar na ?asa Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawarshi da manema labarai a garin Kaduna.

Imam Bala Lau ya kara da cewar matakin da gwamnatin Kano ta ?auka abin a yaba ne, kuma zai taimaka wajen kawo karshen ya?uwar irin wadannan miyagun maganganu a tsakanin Musulmi.

“Irin wannan mataki ne Gwamnatin Jihar Neja ta ?auka akan wani Mutum da ya fito yana miyagun maganganu akan Sahabban Manzon Allah SAW inda aka ?auki matakin da ya dace domin samun zaman lafiya.

Dangane da halin da tsaro ya shiga ciki musamman a yankin Arewacin Najeriya, Imam Bala Lau ya ce tuni ?ungiyar Izala ta yi nisa wajen gudanar da da’awa da wa’azuzzuka a dazuka da rugagen Fulani a wasu Jihohin Arewacin Najeriya, jihohi irin su Adamawa, Katsina, Zamfara da Kebbi, domin Ilimantar da Fulani hasken ilimin addini, wanda Malaman ?ungiyar ke gabatarwa cikin harshen Fulantaci.

Inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa himma wajen sake farfa?o da ilimin ‘ya’yan Makiyaya, domin kawar da jahilci a tsakanin su, kasancewar Jahilci ne ?ashin bayan dukkanin wasu fitintinu dake faruwa a ?asar.

Imam Abdullahi Bala Lau ya kuma yaba kokarin da Dr. Ahmad Gumi ke yi na shiga cikin dazuka da ganawa da ‘yan bindiga domin samar da sulhu, inda ya ce wannan mataki ne mai kyau, amma Ilimantar da su wani muhimmin abu ne, muddin aka samu ilimi babu shakka ta’addanci zai kau, amma idan ya zamana babu ilimi ko da an yi sulhu da ‘yan bindiga suna iya sake komawa cikin fitina.

Shugaban na Izala ya kuma yi kira ga dukkanin jama’ar Najeriya da su dage wajen yin addu’o’i ga Allah SWA domin samun zaman lafiya a Najeriya da kawar da dukkanin wasu matsaloli da ke addabar ?asar.

Related posts

One Thought to “Izala Ta Goyi Bayan Zaman Mukabala Tsakanin Abdul-Jabbar Da Malaman Kano”

  1. […] Izala Ta Goyi Bayan Zaman Mukabala Tsakanin Abdul-Jabbar Da Malaman Kano […]

Leave a Comment