Gyaruwar Najeriya: Muna Bukatar Shugaba Mai Tabin Hankali – Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce Nijeriya na bukatar shugabanni masu ɗan taɓin hankali da za su iya mai da kasar kan turba mai dorewa.

Obasanjo ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban Nijeriya karkashin jam’iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen a Abeokuta, a gidansa da ke Ogun.

Obasanjo yace yana bakin ciki akan halin da Nijeriya ke ciki ba wai kawai koma bayan ba ne gare shi, da kuma wadanda suka damu da Nijeriya baki daya.

Tsohon shugaban ya jaddada cewa, Nijeriya za ta iya kawo karshen matsalar tsaron da take fama da ita cikin shekara biyu in ta samu shugaban da ya dace wanda kuma yake fatan daukar matakan da suka dace.

Obasanjo yace yanzu Nijeriya na bukatar shugaba mai dan tabin hakali ne wanda zayyi aikin ba sani ba sabo domin maido da Kasar cikin hayyacin ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply