Fina-Finai: Mazinata Na Kai Mini Hari A Kannywood – Jaruma Nafisa Salisu

A tattaunawar da Jaridar Lerdership Hausa ta yi da Jarumar masana’antar Kannywood Nafisa Salisu ta bayyana nasarori da ƙalubalen da ta ke fuskanta a cikin masana’antar.

LEADERSHIP A YAU: mai karatú zai sò jin wacece Nafisat Salisu?

NAFISA SALISU: to ni dai an haifeni a wata Unguwa a cikin garin Kanø sannan na yi makarantar firamare gami da sakandire a Edcellence Classic Gollege dake Unguwar Hotoro, duk da dai iyayena ba ‘yan Jihar Kano ne su ba, ‘yan Jihar Kogi ne wanda kuma kasuwanci ya kawosu nan, sannan ni yaran IGALA ce, bayan na kammala sakandire ne kuma na fara sha’awar shiga harkar fim a inda na samu nasarar shiga a 2017, da kuma yaddar iyayena.

LEADERSHIP A YAU: Ta hanun wa ki ka shigø masana’antar kannywood?

NAFISA SALISU: eh to gaskiya farko Ali Gumzak na fara sa ni a masana’antar Kannywood sakamakon muna catin da shi a Facebook kuma ina nuna mishi sha’awata na son shiga masana’antar Kannywood.

LEADERSHIP A YAU: Wane kalubale kika fuskanta farkon shigowarki?

NAFISA SALISU: uhmm (dariya) gaskiya na ci karo da masu nuna sha’awar lalata da ni. Sannan kuma duk wanda ya nunan haka a matsayina na wacce na shigo harkar ka ga ba zai yiwu mutum ya nuna mun ga irin abinda ya ke so da ni kawai na fito nayi masa rashin kunya, kawai dai ina fitowa na gayawa mutum cewa kawai kayi hakuri ni ba na irin wannan harkar sannan ba dan ita na shigo Kannywood.

LEADERSHIP A YAU: Duba da yanda yanzu masana’antar kusan kacokam ta koma yin finafinai masu dogon zango (series) shin ko kema kina irin wadannan fina-finan?

NAFISA SALISU: Ina yin mai dogon zangø ga duk masu bibiyar SIRRINSU MEDIA nice nake jan ragamar fim din mai suna ‘MACEN SIRRI’ ana kira na Sarauniya.

LEADERSHIP A YAU: Yawanci idan aka mace tana fim ana yi mata wani kallø na daban ko kin fuskanci wannan matsalar?

NAFISA SALISU: bazance ba ayi ba amma dai ni gaskiya bań fuskanci haka ba hasalima duk inda na shiga zaka ji ana kiranà da sunan MACEN SIRRI ko SARAUNIYA abin ma bai yi yawa anan na fara jin abinda wadanda suka shahara suke ji.

LEADERSHIP A YAU: Shin Nafisa tana da aure?
NAFISA SALISU: A’a ba ni da aure kuma ban taɓa yi ba amma ina da niyyar yi Insha Allahu.

LEADERSHIP A YAU: Bayan harkar Fim akwai wata sana’a da kike yi?

NAFISA SALISU: Ina aikin gyaran gashi da kuma yin dinki damań kuma shi na gada daga gurin mahaifiyata.

LEADERSHIP A YAU: Da me za ki karkare a karshe?

NAFISA SALISU: To a karshè ina yiwa Maigidana Maje El-Hajeej Hotoro wanda shi ya fito da ni duniya ta san ni, ya koya min aikin jarida ya sa ni a fim din Macen Sirri duk da kushe da hassada da akè ta yi wai ban dace da na jagoranci fim din ba. Bai taba nuna sha’awar lalata da nib a, ya dauke ni kamar ‘yar uwarsa ya taimake ni ya kai ni inda ban yi zato ba a rayuwa, na san mutane da dama saboda shi.

Sannan ina yi wa masoyana fatan alkairi tare da yin kira ga jarumai irina masu tasøwa musamman yadda wasu sùke yiwa manya rashin kunya wato ina nufin wadanda suka dade a cikin wannan masana’antar sabida rashin kunya ba abune mai kyau ba kuma koda ace a yanzu ka fisu samun wani abu mutum yana tunawa suma a lokacinsu suma sun samu karbuwa yadda suka ja baya to kaima wataran haka zaka koma kuma duk abinda mutum yayi sai anyi masa idan kuma aka yi ma bai zama lalle ka ji dadi ba. Na gode.

Labarai Makamanta

Leave a Reply