Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kula da almajiranci.
Majalisar wakilai ta Najeriya ce ta fara amincewa da dokar kafin ta kai gaban shubaban, inda ya ratta?a mata hannu.
Dokar dai na neman samar da tsarin ilimi mai kyau da bunkasa fasahar koyon sana’o’i da kuma rage talauci tsakanin almajirai a Najeriya.
Har ila yau, dokar za ta kuma kyautata karatun tsangaya da rayuwar almajirai da sauran yaran da ke gara-ramba ba su zuwa makaranta.
Harkar Almajiranci wani al’amari ne da ya da?e yana ci wa gwamnatin da sauran jama’a tuwo a kwarya, hakan ya biyo bayan yadda aka sauya akalar Almajirancin zuwa wani yanayi na barace barace da sauran abubuwa da suka yi hannun riga da karantawar addini.