Mukadashin Sufeta Janar na Yan sandan Nigeria, Usman Baba, ya ankarar da kwamishinonin babban birnin tarayya Abuja da jihar Plateau kan yiwuwar hari daga yan kungiyar Boko Haram, The Punch ta ruwaito. Kwamishinan ya sanar da su ne cikin wata sako da ya aike wa kwamishinonin biyu mai dauke da sa hannun babban jami’insa, Idowu Owohunwa mai mukamin mukadashin CP.
Ya ce bayannan sirri sun nuna cewa yan ta’addan suna shirin kai hari a Abuja da Jos. Sakon mai lamba TB: 0900/IGP.SEC/ABJ/VOL.TI/47 an mata lakabi ne da ‘Yan ta’adda za su fadada harinsu.’ Wakilin ya samu kofi na sakon a ranar Juma’a. A cikin sakon, mukadashin na IGP ya umurci kwamishinonin yan sandan su yi bitar tsarin tsaronsu su kuma tsaurara matakan tsaro musamman a gine-ginen gwamnati a Abuja da Jos.
“Bayannan sirri da sufeta janar na yan sanda ya samu ya nuna yan ta’addan Boko Haram na shirin kai hari a manyan birane a kasar, musamman a Jos, Plateau da FCT, Abuja.
“Wadanda za su jagoranci kai hari sune Muhammad Sani, kwamandan Boko Haram da ke zaune a dajin Sambisa da mataimakinsa, Suleiman, wanda ke buya a Lawan Musa Zango, Gashua, jihar Yobe. “Don haka, Sufetan Janar na yan sanda na umurtar ku da kuyi bitan tsarin tsaronku musamman kusa da gine-ginen gwamnati da ke yankunanku domin kare afkuwar mummuna shirin yan ta’addan.”