Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan bindiga sun kashe wani mutum da suka sace bayan sun karbi naira miliyan daya a matsayin kudin fansa daga yan uwansa a garin Rigachikum dake yankin ?aramar hukumar Igabi.
A watan Fabrairu ne yan bindiga suka farmaki gidan mutumin a yankin Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi sannan suka sace shi da wasu a yankin ciki harda mai shirin zama Amarya.
A yayin mamayar, an harbe wani jami’in kwastam da ke aiki da FOU Zone B, Kaduna sannan daga bisani ya mutu a asibiti. Wata mata a yankin ta shaida wa manema labarai mutuwar mutumin ya zo ne a daren Talata bayan yan uwan marigayin sun kai ma yan bindigar kudin fansa.
“Sun harbe shi bayan sun karbi kudin fansa daga mutumin da ya kai masu kudin. Dukkanin mazauna yankin na cikin alhini bayan sun sami labarin mutuwar.” An tattaro cewa an yi jana’izar mutumin a garin Unguwar Shanu inda iyalansa ke da zama.
Rahotanni sun bayyana cewar har yanzu amaryar da wani mutum daya suna a hannun wadanda suka yi garkuwa da su din.
Ayyukan ‘yan bindigan na cigaba da ?amari a yankuna daban daban dake fa?in jihar, inda a tsakiyar makon nan da muke ciki ‘yan Bindigar suka kai wani mummunan hari a yankin kudandan dake karamar hukumar Chikum inda suka kashe mutane da sace wani malamin addinin Kirista.