Babu Dan Bindigar Da Zai Saura A Zamfara – Matawalle

Rahotanni Daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya ce ‘yan bindiga sun yi watsi da damar da suka samu ta sulhu a baya, yanzu tsakanin gwamnati da su sai aikawa lahira.

Cikin wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga Gwamna Matawalle yana jawabi a wani masallaci bayan idar da sallah, inda yake yi wa al’umma bayani kan halin da ake ciki a jihar.

Matawalle ya ce “gaskiyar magana suna shan wuta sosai, ko jiya an turo kwamiti babba a sameni, cewa in tsagaita don Allah, in saki a rika samun abinci na ce wallahi ba zan saki ba,”.

“Duk wani abu da Allah ya ce muyi munyi, saboda haka mun yi iyakar yinmu, yanzu abin da muke yi shi ne mu sada su da ubangijinsu su amsa tambayoyi ga Allah.”

A watan Fabirairu, Gwamnan ya ce sulhu da ‘yan bindigar ne zabi na karshe da ya rage domin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

Amma a yanzu Gwamnan ya ce matakin yakarsu ba dare ba rana suka dauka domin sun ki amfani da damar da aka ba su.

Ya rarrashi mutanen jihar da su yi hakuri game da datse layukan waya da aka yi a fadin jihar, an yi ne domin samar da zaman lafiya mai dorewa ga al’ummar jihar Zamfara.

Matawalle ya ce in Allah ya yarda Zamfara za ta samu lafiya, don haka a shirye yake ya sha walaha tare da mutanen jihar domin a gudu tare a tsira tare.

“Idan aka daina shigar da abinci da itace da man fetur da kuma amfani da babura ‘yan bindigar za su fito su rika mika kansu da kansu.

“Yan siyasa su ji tsoron Allah su daina sayan babura suna raba wa mutane, wadanda su kuma daga baya suke sayar wa wadannan miyagu.” in ji Matawalle.

Labarai Makamanta

Leave a Reply