Ba Kashe Shi Aka Yi Ba, Rasuwar Iyan Zazzau Ta Allah Ce – Iyalanshi

Daya daga cikin iyalan marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo na cewa kashe marigayi Iyan Zazzau aka yi wanda ke shari’a da gwamnatin jihar Kaduna kan zabar sarkin Zazzau na 19 da aka yi a shekarar da ta gabata ta 2020.

Jim kadan bayan sanar da labarin mutuwarsa a Kaduna a ranar Juma’a, sai jita jita ta fara yawo a jihar cewa an kashe marigayi Iyan Zazzau ne domin ƙalubalantar naɗin Sarautar sabon Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli da ya ke yi a Kotu.

Sai dai da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan binne marigayin, Shehu Iya Sa’idu wanda ke rike da mukamin Tafidan Dawakin Zazzau kuma dan marigayi Iyan Zazzau ya ce jita jitan kisan bai da tushe.

Ya kara da cewa kasancewarsa daya daga cikin makusantan marigayin, yana iya tabbatar da cewa mutuwar Allah da Annabi marigayin yayi.

“Ya yi fama da rashin lafiya, amma saboda shi mutum ne mai jarumta, mutane da dama basu san da hakan ba face mu da muke kusa da shi,” in ji shi.
“Jita jitan harbi ba gaskiya bane kuma ina daya daga cikin makusantanshi saboda mahaifina ne ya rike shi sannan shima ya rike ni tun ina shekaru biyu. “Don haka ina iya fada maku cewa lokacinsa ne yayi kuma Allah Ubangiji wanda ya bamu shi ya karbi abinsa.
“Addu’anmu shine Allah ya yi masa rahama sannan ya bashi Alhannah Firdausi.”

Sa’idu ya ƙara da cewar an dawo da mahaifin nasa gida domin a binne shi saboda ya bar wasiyyan cewa a yi masa jana’iza a masallacin Juma’a na Sabon Gari.

“Muna yi wa Allah Madaukakin Sarki godiya da ya bamu ikon sauke wannan nauyi na wasiyya da bayar,” in ji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply