Ba A Taba Yin Shugaba Mai Hakuri A Najeriya Kamar Buhari Ba – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa shi dai har yanzu bai taba ganin wani Shugaba mai hakuri irin shugaba Muhammadu Buhari ba a gaba daya tarihin Najeriya.

Ministan wanda yayi magana ranar Juma’a yayinda ya karbi bakuncin tawagar wakilan gammayar kasashen Afrika (AUDA-NEPAD) da (APRM) a ziyarar da suka kai ofishin shi dake Abuja.

Lai Mohammed yace dubi ga irin dimbin kalubalen da Najeriya ke fama cikin shekaru shida da suka gabata, ana bukatar hakuri da azanci. Yace: “Jagoranta kasa irin Najeriya kamar wata karamar duniya ce kuma shi yasa nike girmama hakuri, azanci da salon shugabancin shugaban kasa.”

“Abinda yasa na fadi haka shine cikin shekar shida da suka gabata, ina halartan taron majalisar zartaswa.” “Akan ko wani lamari, shugaban kasa na sauraron dukkan Ministoci 43 inda suna son tsokaci.” “Duk da cewa mun san shirme wasu ke fada cikin Ministocin, shugaban kasa zai sauraresu kuma yace ‘Nagoda’ a karshe.”

Ministan ya kara da cewa “har yanzu ban ga shugaba mai hakuri da fahimta irin Shugaba Muhammadu Buhari ba a tarihin Najeriya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply