An Shawarci Gwamnonn Arewa Da Su Faɗaɗa Tattaunawar Su Da ‘Yan Bindiga

Shugaban kamfanin sadarwa na EasyGIS kuma kwararen masanin harkokin siyasa Malam Ibrahim Hussein Abdulkarim ya bukaci gwamnonin shiyyar arewa da su fadada tattaunawar da suke yi da ‘yan bindiga domin samun sahihiyar mafita kwara daya da data kawo karshen matsalar tsaron da ta addabin yankin na arewacin Nijeriya,

Malam Ibrahim Abdulkarim ya bayyana hakanne a yayin da yake Hira da gidan Rediyo Talabijin na Liberty dake Abuja a cikin shirin Ina Dalili,

Ibrahim Abdulkareem ya kara da cewar bayani akan cewa sulhu abune mai asali a tarihinmu domin warware matsaloli ko sabani a tsakanin al’umma, ya kuma nuna tababa kan yadda ake baiwa ‘yan bindiga kudade hakan bazai hanasu aikata abunda suke yi ba, ya kuma nanata muhimmancin dake akwai na gayyato illahirin shuganannin addinai dana al’umma kai har da ‘yan majalisa wadanda dune wakilan jama’a don bada tasu gudumawar a kokarin wanzar da zaman lafiya

Ya kuma bayyana muhimmancin dake akwai na samun lokaci guda inda Gwamnonin Arewa dana Kudu za su tattauna tare da yin muhawaraawara akan gwanonin jihohi na arewa dana kudu za su ware lokaci guda domin hada karfi da karfe wuri guda da summary lalubo bakin zaren rikicin makiyaya da manona wanda me bycigaba da haifar da cece-kuce a tsakanin al’ummar kasar nan,

Daga karshe ya nuna takaicinsa kan yadda hukumar nan ta wayar da kan ‘yan kasa wato NOA ta kasa kasau na sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya wajabta mata na wayar da kan ‘yan kasa da tarbiyantar dasu kan manofofin gwamnatin tarayya na wanzar da zaman lafiya da Cigaban kasa

Labarai Makamanta

Leave a Reply