Akwai Laifin ‘Yan Najeriya A Matsalar Tsaron Da Ake Ciki – Na’Allah

Sanatan mai wakiltar Kudancin jihar Kebbi, ya yi kira ga sauran mutanen Najeriya su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen samar da zaman lafiya. Bala Ibn Na’Allah ya bayyana wannan ne jim kadan bayan ya gana da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa a jiya.

Ɗan majalisar Dattawan ya bayyana cewa ya ziyarci fadar Shugaban ƙasa ne domin ya yi zaman da ya saba yi da Buhari a kan sha’anin kasa. Sanata Bala Na’Allah bai yi bayani ko ya kai wa shugaban kasar ziyara ne da sunan ‘yan majalisa ba.

Da aka tambaye sa abin da ya kawo shi, sai ya ce sun yi magana gar-da-gar da shugaban Najeriya a kan yadda za a shawo kan matsalar rashin tsaro. Na’Allah ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin nan da gaske ta ke wajen kawo zaman lafiya, ya ce dole ne mutane su ba hukumomi goyon-baya.

A game da abin da ya sa matsalolin kashe-kashe suke kara bayyana har kullum, ‘dan majalisar yake cewa su ma al’umma su na da irin na su matsaloli. “Boko Haram suna Arewa maso gabas ne, ‘Yan bindiga suna Arewa maso yamma. Wadannan duk rashin adalcin da mu ka yi a baya ne ya jawo mana su.”

“Abin takaici ne dai sai da gwamnatin nan ta zo wadannan abubuwa suke bayyana, shiyasa ba gwamnati ce ta ke da alhakin matsalar kai tsaye ba.” Bayan an kashe mutum sama da 2,

Labarai Makamanta

Leave a Reply