A Shirye ‘Yan Bindiga Suke Su Ajiye Makamai – Tsohon Shugaban Inshora

Tsohon shugaban hukumar inshoran lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf, yace ‘yan bindiga na buƙatar tattaunawar zaman lafiya da malamai, saboda haka a shirye suke su watsar da makamansu domin rungumar zaman lafiya.

Usman Yusuf ya bayyana cewa ya fahimci haka ne a taron da suka yi da yan bindigan kala daban-daban a cikin ayarin da ya kasance a ciki ƙarkashin jagorancin Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi.

Yayin da yake jawabi a wata tattaunawa da yayi da gidan talabishin na Arise Tv ranar Talata, Yusuf yace: “Wannan shine abinda muka gano a dukkan jihohi biyar da muka je, yan bindigan suna son sauraron malamai.

A jihar Neja sun tattaro kwamandoji daga jihohi biyar, kuma sun saurari malaman da muka je dasu.” “Da alama su kansu sun gaji da wannan mummunan aikin da suke aikatawa, suna buƙatar tattaunawa da malamai domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa.”

“Akwai rawar da jami’an tsaro ke takawa sosai, domin idan da babu jami’an tsaro da yanzun Boko Haram ta ƙwace yankin arewa maso gabas ya koma ƙarƙashinsu.” “Hakanan da yanzun yan bindiga sun kwace arewa ta tsakiya, saboda haka akwai rawar da jami’an tsaro ke takawa, amma duk wanda yace maka za’a warware wannan matsalar da ƙarfi to tabbas bai san yadda abin yake ba.

“Bazai yiwu a warware wannan matsalolin da karfi ba, bai kamata mu cigaba da saka bam ga mutanen da yakamata ace mun gyara rayuwarsu ba.” Inji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply