Adamawa: PDP Ta Gudanar Da Zaben Shugabanni

A yau ne dai jam iyar P D P a jahar Adamawa ke gudanr da taron zaben sabbin Shuwagabannin wadanda zasu jagoranci ragamar jam iyar na tsawon shekaru hudu masau zuwa.

Da yake kada nashi kuri ar kuma shine na farko fara zabe gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya baiyana farin cikinsa da kuma jin dadinsa dangane da wannan zabe na sabbin ahuwagabannin jam iyar.

Gwamna fintiri yace yana fatan wannan zaben zai taimaka wajen cigaban jam iyar yadda yakamta a fadin jahar don haka akwai bukatar samun hadin kan membobin jam iyar ta P D P a fadin jahar wanda acewarsa hakan zai kai jam iyar ga samun nasara a koda yaushe.

Kuma yayi fatan za a kammala taron lafiya ba tare da wata matsalaba.

Shima anashi jawabi tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ahima nuna gamsuwarsa yayi da yadda aka shirya taron zaben sabbin shuwagabannin jam iyar, ahima shawartan yan jam iyar yayi da su kasance masu kansu da kuma baiwa shuwagabanin jam iyar hadin kai da goyon baya domin samun cigaban jam iyar yadda ya kamata.

Wakilai dubu biyu da dari shida da goma sha hudu ne dai wadanda suka fito daga sassa daban daban dake fadin jahar Adamawa ne zasu yi zaben shuwagabanin jam iyar a matakin jahar.

Yan takara da yawansu yakai talatin da tara ne dai aka tantance domin neman mukamai daban daban a jam iyar ta P D P.

Kum taron na gudanane a dandalin Mahmudu Ribadau dake yola cikin tsauraran mataken tsaro.

Kuma taron na gudana ne a dan

Labarai Makamanta

Leave a Reply