Labarin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka bayan da wata babbar motar dakon kaya ta kufce ta faɗa kan mutane a garin Jimeta.
Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa mutum 11 ne suka mutu nan take sakamakon hatsarin.
Sai dai shugaban Hukumar kare afkuwar haɗurra ta Najeriya reshen jihar Adamawa ya ce gaba ɗaya mutane 15 ne lamarin ya rutsa da su.
Ya ƙara da cewa sun gano cewa lalacewar burki ne ya haifar da haɗarin.
Motar ta ƙwace ne ta haye kan wasu motoci kafin ta faɗa wani garejin kanikawa a mahaɗar Vunoklang.
Rundunar ƴan sanda a jihar ta Yola ta ce an kai mutanen da suka samu raunuka asibiti.