Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga shugabanni na kananan hukumomi, jihohi da tarayya da su tabbatar da wanzuwar adalci da daidaito domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’ar kasar nan.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne yayin bikin bude masallacin Juma’a da ke fadar Osana na Keana da ke karamar hukumar Kena ta jihar Nasarawa a ranar Juma’a.
Sa’adu Abubakar wanda shine shugaban majalisar koli ta al’amuran addinin Musulunci a kasar nan ya ce, “Ina kira ga ‘yan Najerta da su guji hada al’amuran siyasa da addini kuma su cigaba da yi wa shugabanninsu addu’a.
“Ina jinjinawa jama’a karamar hukumar Kaena a kan zaman lafiyar da suka runguma duk da banbance banbance addini dake tsakanin su.
“Ina kara kira da a saka darussan tarihi a makarantu domin a samu abin sanar da ‘yan baya a kan zaman lafiyar da magabatansu suka yi,”.
A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya jinjinawa Sarkin musulmin a kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da haɗa kan jama’ar ƙasa.