Ɓatanci Ga Annabi: Kotu Ta Umarci A Saki Mubarak Da Biyanshi Diyya

Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin sakin Mubarak Bala, wanda ya yi amfanin da shafinsa na Facebook ya wallafa wasu rubutu dake nuna batanci ga Annabi Muhammad (SAW) sannan Kotun ta buƙaci a biya shi diyya na ɓata mishi lokaci da aka yi.

An kama Mubarak Bala ne a watan Fabrairu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

‘Yan sandan jihar Kaduna suka kama shi sannan daga bisani aka mayar da shi hannun yan sandan jihar Kano a ranar 2 ga watan Mayun 2020.

Da ya ke yanke hukunci kan karar da lauyoyin Bala suka shigar na zargin keta hakkinsa na bil adama, Mai shari’a Inyang Ekwo ya ce tsare Bala da ‘yan sanda suka yi na tsawon watanni ya keta hakkinsa na ‘yanci, adalci, zirga-zirga da ‘yancin tofa albarkacin bakinsa.

“Rashin barin wanda ake zargi ya gana da lauyoyinsa keta hakkinsa na adalcin shari’a ne da samun lauya kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 34 da 35(2) a karkashin kudin tsarin kasa ta 1999.”

Alkalin ya kuma umurci rundunar ‘yan sanda su biya naira 250,000 ga wanda ake yi karar, ba tare da bata lokaci ba.

Mubarak Bala ya dade yana sukar addini musanman Annabi Muhammad SAW, tun bayan ridda daga addinin musulunci da yayi a shekarar 2014.

An kuma gano cewar iyayensa sun taba kai shi zuwa asibitin kwakwalwa a kan tilas a Kano amma daga bisani aka sako shi kuma tun lokacin ya cigaba da samun barazanar kisa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply