‘Yan Bindiga: Za A Tsaurara Tsaro A Hanyar Abuja-Kaduna

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta ce za ta tura ƙarin dakaru don kyautata tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Matakin ya biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasa, inda suka kashe mutum aƙalla takwas da raunata wasu 41 sannan suka sace wasu da dama a yammacin Litinin da ta gabata.

Wani saƙo ɗauke da hotuna da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna dakarun jere a kan layi.

“Dakaru sun shirya tsaf don tura su aiki na musamman a kan hanyar Abuja-Kaduna. Ana yi musu jawabi a hedikwatar ‘yan sanda ta ƙasa kafin su fita ” in ji Mista Adejobi.

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya kai ziyara wurin aikin da ake yi na gyara layin dogon da ‘yan bindigar suka ragargaza da bam a harin na ranar Litinin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply