Son Kai Da Hassada Sun Fi Muni Akan Zina Da Luwadi – Lamido Sunusi

IMG 20240409 WA0041

Muhamadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14, ya ce kwadayi, son kai da hassada “su ne manyan zunubai” fiye da zina da luwadi da caca.

Sanusi ya yi magana ne a ranar Lahadin da ta gabata a matsayin bakon malami yayin wata lakca ta watan Ramadan mai taken “Wasu bangarori na manufar ibada”.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN ya ce wani bangare na dalilin da ya sa ake samun tabarbarewar zamantakewa a kasar nan shi ne yadda wasu Musulmi suka manta da cewa za su ba da labarin abin da suka aikata a gaban Allah.

Ya ce mutane suna yin sallah kuma suna azumi amma suna ci gaba da aikata munanan ayyuka “saboda zukatanmu ba na Musulunci ba ne”.

Sanusi ya yi zargin cewa wani gwamnan jihar da ke aiwatar da Shari’ar Musulunci a Najeriya ya saci kudi ya sayi otal a Legas.

Duk da yake bai ambaci sunan gwamnan ba, Sanusi ya ce jiharsa ta kasance “mafi girman misali na ci baya”.

Masanin tattalin arzikin ya ce da shugabannin sun san cewa za su bayyana amanar da aka ba su, ba za su saci dukiyar al’umma ba.

“A tsarin zamantakewa da ibada, kun san lokacin da zukatanmu ba su da kyau, ayyukanmu ba za su yi kyau ba,” in ji shi.

“Muna cewa mu musulmi ne, muna zuwa masallaci muna yin sallah, kuma Allah ya ce salla tana hana ayyukan alfasha da munanan ayyuka. Me ya sa muke zuwa yin sallah kodayaushe, muna yin azumi kullum sannan muna aikata wannan mugwayen dabi’u?

“Ta yaya za ka samu musulmi ya zama minista ko gwamna, abin da yake tunani shi ne yadda zai saci dukiyar al’umma ya gina wa kansa babban gida ko ya yi tarawa ‘ya’yansa biliyoyin ya han mutane?

Idan kun san abin da Annabi ya ce game da shugabanci. Amana ce kuma a ranar kiyama za ta zama abin bakin ciki, da nadama, ga wadanda ba su rike wannan amana yadda ya kamata ba. Uh

Labarai Makamanta

Leave a Reply