Shugabancin Mala Buni A APC Abin A Yaba Ne – Jigon APC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jigon jam’iyyar APC, Hon. Patrick Obahiagbon ya shawarci shugaba Buhari da shugaban kwamitin shirya taron gangamin APC Mai Mala Buni kan shirya hanya dodar ga zaben 2023.

Hon Obahiagbon, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne ya yi wannan batu ne a ranar Litinin a Abuja, a wata wasikar yabo da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni.

Tsohon dan majalisar ya kara da cewa kada muradin kashin kai da son kai su wuce muradun jam’iyyar. Hakazalika, ya koka kan yadda jam’iyyar ke fuskantar barazana da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da yace ya kamata a kawo karshensa.

A bangare guda, ya bayyana ra’ayinsa da cewa, Mai Mala Buni ya dawo da jam’iyyar APC kan turba, duk da samun rikice-rikice daga mambobin jam’iyyar mabambanta a baya.

Hon Obahiagbon ya ce salon jagoranci mai ban sha’awa da tsarin tuntuba daga Buni baya ga tawali’u, hadin kai tare da matsayi da kuma kwarewar hulda tsakanin mutane ya haifar da ɗa mai ido ga jam’iyyar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply