Najeriya Na Neman Daukar Bakuncin Gasar Kofin Afirka 2025

Najeriya da Benin sun mika takardar hadin gwiwa domin daukar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 2025.

Hakan ya nuna za su yi hammaya da Aljeriya da Maroko da kuma Zambia domin neman basu damar daukar bakuncin gasar.

Najeriya wacce ta lashe gasar kofin Afcon sau uku na neman sake daukar bakuncin gasar bayan ta yi hakan a 1980 da kuma hadin gwiwa tare da Ghana a 2000.

“Bayan kammala dukkan abubuwan da suka wajaba, mun mika takardar neman izini a wajen hukumar kwallon Afrika – Caf kafin cikar wa’adin na 16 ga watan Disamba,” in ji wanni babban jami’in hukumar kwallon Najeriya – NFF.

“NFF za ta kara bayar da wasu bayannan a makonnin da ke tafe.”

Najeriya ta lashe gasar a Lagos shekaru 42 da suka wuce sannan kuma ta sha kashi a wasan kashe tsakaninta da Kamaru a shekara ta 2000.

Labarai Makamanta

Leave a Reply