Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Gargadi Masu Hankoron Gudanar Da Zanga-Zanga

IMG 20240225 WA0030

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci ‘yan ƙasar da kada su yi zanga-zangar nuna ɓacin rai da matsin rayuwa a wata mai zuwa, kamar yadda Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya bayyana.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasar a yau Talata, ministan ya ce Tinubu ya buƙaci masu shirya zanga-zangar da su dakata tukunna.

“Game da maganar zanga-zanga, shugaban ƙasa ya ce babu buƙatar yin ta tukunna,” in ji shi. “Ya nemi su jingine batun, ya nemi su jira su ji martanin da zai mayar game da ƙorafe-ƙorafensu.”

Zanga-zangar da wasu ke shiryawa domin nuna damuwarsu kan halin matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki na cigaba da samun karɓuwa a shafukan sada zumunta, kuma suna sa ran gudanar da ita a farkon wata mai kamawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply