Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci: Turji Na Da Ciwon Hauka – Bello Matawalle

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Najeriya Bello Matawalle ya yi watsi da zargin da fitaccen ‘dan ta’adda Bello Turji ya masa na kawar da kai wajen yaki da ta’addanci lokacin da yake rike da kujerar gwamnan Zamfara.

Turji ya danganta karuwar ayyukan ‘yan bindiga a jihar da kuma makwabtanta da manufofin gwamnatin Matawalle, inda ya bayyana cewar mazauna Shinkafi da Zurmi da kuma Isa dake Sokoto na da masaniya a kai.

A martanin da ya gabatar ta hannun Dayemi Saka, Matawalle ya bayyana zargin a matsayin wani yunkuri na kawar masa da hankali daga ayyukan da yake yi.

Matawalle ya bayyana Turji a matsayin mai fama da tabin hankali wato ciwon hauka da ba za’a iya sauraron maganarsa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply