Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF) ta bayyana cewa ɗaukar nauyin sukar ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle da babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, wani yunkuri ne na sukar shugaba Tinubu.
Kungiyar ta bayyana cewar a fili yake kwanan nan an ga Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya fito ta kafar talabijin na Channel yana bayyana cewar wai shugaban ya gaza wajen samar da tsaro ba jihar Zamfara da yankin Arewa.
Hakazalika Gwamnan Lawal ta hannun kungiyoyin da ya ɗauki nauyin su, sun fito suna sukar ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle da babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, yana kiran cewa sun cancanci a kore su daga muƙamansu, wanda hakan kowa ya sani ana harin Tinubu ne kasancewar su amintattun sa ne.
A cikin wata takardar sanarwa da shugaban kungiyar Matasan na ƙasa Alhaji Yerima Shettima ya fitar a Kaduna, ya bayyana Gwamnan na Zamfara a matsayin wanda ya gaza wajen sauke nauyin da ke a kanshi na matsalar tsaro dake addabar Jihar shi, abin mamaki a ranar da ‘yan Bindiga suka yi garkuwa da dalibai mata na jami’ar gwamnatin tarayya dake Gusau, a wannan ranar ce gwamnan ya shilla zuwa Amurka wasu sabgogi ya yi watsi da Jihar shi.
“Zuwan Gwamnan ƙasar Amurka a daidai lokacin da Jihar shi ke cikin halin matsala ta talauci da rashin tsaro abin takaici ne matuka”
Shettima ya ƙara da cewar a fili yake Gwamna Lawal yana haifar da tarnaki wajen samar da tsaro a jihar, inda ya yi ƙememe da haɗa kai da jami’an tsaro na gwamnatin tarayya wanda hakan ya haifar da matsala sosai”
“Kowa ya gani a a faifan wani bidiyo da ya bayyana an ga ‘yan Bindigar na neman yin sulhu da shi”.
“Babu shakka kokari da kwazo na ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle da babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, wanda ya taimaka wajen samar da hadin kai a tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaro, wanda hakan ya taimaka gaya wajen karya laggon matsalar tsaro a faɗin ƙasar gaba ɗaya.
Daga karshe Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa Tinubu da cewar ya yi watsi da kiraye kirayen ‘yan gaza gani masu kiran ya sauya Bello Matawalle da Nuhu Ribadu, domin amintattu ne kuma jajirtattu ne akan ayyukansu.