Na Yafe Wa Budurwar Da Ta Zage Ni – Sheikh Daurawa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Shiekh Aminu Daurawa, ya yi tsokaci kan wa’azinsa da ya haddasa cece-kuce a kwanan nan.

Daurawa ya bayyana cewa bai yi wa’azin domin cin zarafi ko mutuncin wani ba, ya ce wa’azi ne da aka yi domin jan hankalin al’umma a kan duniya da kuma rudin da ke cikinta. Hakazalika ya ce babu batsa a cikin kalamansa domin bayani ne ya dauko wanda Sayyidina Ali ya yi.

Sheikh Daurawa ya kuma ce ya yafewa budurwar da aka ce ta zage shi kan haka tun ma kafin ta nemi yafiyarsa.

“Ban so na yi magana a kan wannan matsala ba saboda gani nake yi kamar ta wuce. To amma abubuwa guda uku ne zai sa dole nayi magana a kai kamar yadda yan uwa suka bukata.

“Na farko shine a cikin karatun da nayi ba inda aka yi batsa, babu kuma inda aka ci zarafin kowa. Karatu ne a kan duniya, malamai suna so su fadakar da mutane a kan duniya da yadda take halakar da mutane da zubar da jini, da ta’addanci, da kashe-kashe, da garkuwa da mutane, da kashe kananan yara duk ana yi ne saboda duniya.

“Sai malamai suka tashi su bayyanawa mutane duniya da yadda take da kuma illar shagala da duniya har a kai ana zubar da jini a kai. Don haka Sayyidina Ali shi ya yi wannan bayani ni kuma na dauko shi a cikin wannan tafisiri na kurtubi.

Kuma duk malamai sun gani a cikin tafsirin suratul Hadid, don haka ba batsa bane, ba cin fuska bane. “Manyan malaman Supaye sun kawo a litattafansu, manyan malaman ahlu sunnah ma sun kawo, manyan malaman shi’a suma sun kawo a litattafansu, saboda haka ba batsa bane ba a kuma yi wannan karatu don cin zarafin wani ba ko cin mutuncin wani ba.

“Na biyu, daga baya ake gaya mun wani bidiyo yana ta yawo wata ta zage ni, kamar yadda mutane suka gaya mun kuma daga baya aka ce ta bayar da hakuri. To ni kafin ma ta bayar da hakurin na yafe mata.

Saboda ni a matsayina na me wa’azi akwai zagi, akwai suka, akwa yabo. Sama da shekara 30 da nake wa’azi na, na ji kalamai masu dadi, na kuma ji kalamai marasa dadi kuma basa damuna.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply