Masu Hankoron A Raba Najeriya Na Cikin Rudu – Sanusi

Tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sunusi na biyu ya bayyana cewa masu Kiran a raba Najeriya suna aikata babban kuskure, kuma tabbas suna cikin rudu.

Khalifan ya bayyana hakan ne lokacin wani biki a Lagos wanda aka shirya domin taya shi murnar cika shekara 60 da haihuwa, Khalifa Sanusi ya ce akwai bukatar kasar ta kasance a dunkule sannan a gudanar da mulki cikin adalci a kasar.

A cikin jawabin nasa tsohon Sarkin na Kano ya kuma nuna takaicin yadda wasu shugabanni a Najeriya ba sa mayar da hankali wajen ilimintar da al’umma.

Kazalika ya Kara da cewa bai wa bangaren ilimi musamman na ‘ya’ya mata muhimmanci shi ne zai kawo ci gaban kasa da kuma bunkasar tattalin Arzika.

Haka Kuma yayi Kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa ilimi musamman a yankunan karkara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply