Kungiyar Dawo Da Martabar Kaduna KRG Ta Yi Gagarumin Taro A Kaduna

IMG 20240412 100425

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar nan mai rajin dawo da martabar Kaduna wato Kaduna Restoration Group a turance ta gudanar da taro a Kaduna tare da shan alwashin taimakawa gwamnatin jihar dama ƙasa baki ɗaya wajen magance matsalar tsaro, tattalin arziki da siyasa.

A cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, sun bayyana cewar manufofin Ƙungiyar shine ganin an samar da kyakkyawan shugabanci da tsaro da samar da hadin kai a tsakanin jama’a domin cigaban ƙasa baki daya.

“Kungiyar za ta samar da wani tsari na tattaunawa a jiha da shiyyoyi domin zaƙulo mafita kan abubuwan dake ci wa Jihar Kaduna tuwo a kwarya da suka shafi rashin tsaro da tauna batun samar da ‘yan sandan jihohi da ake batu akai, da batun sauya tsarin shugaba mai cikakken iko zuwa ga tsarin firaminista, da cin gashin kan kananan hukumomi da samar da sabbin jihohi da batun cire tallafin mai da sauran muhimman al’amura.

Taron na dai ya samu halartar manya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban daban na faɗin jihar Kaduna da kewaye.

Labarai Makamanta

Leave a Reply