Masana tsaro a Najeriya sun ce akwai yiwuwar samun sauki kan matsalar tsaron da arewacin kasar ke fuskanta bayan kisan wasu jagororin ‘yan bindiga da sojoji suka tabbatar da yi.
A ranar Alhamis ne dai shalkwatar tsaron Najeriya ta saki sunayen wasu manyan hatsabiban ‘yan bindiga sha daya da dakarunta suka kashe, bayan jimawa ana farautarsu ruwa a jallo.
Wani dan jarida kuma masani kan kungiyoyin ‘yan fashin daji a Najeriya, ya ce tabbas wannan labari ne mai karfafa gwiwa.
Munir FuraGirke ya shaida wa BBC cewa da zarar an ce an kashe jagoran ‘yan bindiga ko Kacallah kamar yadda aka fi kiransu, to hakan raunana karsashin sauran ‘yan kungiyar ya ke yi.
”Abin kashi biyu ne, akwai bangaren ‘yan Boko Haram, cikin kwamandojin da aka kashe akwai Abu Bilal, da aka fi sani da Al-Furqan wanda shi ke jagorantar bangaren Boko Haram.
Sai kuma bangaren ‘yan bindiga wato barayin daji da suka addabi arewa maso yammacin Najeriya, akwai Haruna Isiya da aja fi sani da Baderi, akwai Damuna, da Alhaji Kacallah Dayi, da Kacallah Idi na mai daro, akwai Kacallah Kabiru mai lakabin Doka, har da Kacallah Azara’ilu na wajen farin ruwa, da Kacallah Baleju da Alhaji Baldu,” in ji Munir.
Munir ya kara da cewa wadannan ‘yan bindiga su na da hadarin gaske, kamar Kacallah Damuna dabar shi a dajin Koli a yankin dan gulbi a masarautar Dan Sadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfar.
Ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a yanki da wasu kananan hukumomin jihar har da wani yanki na jihar Kaduna da Neja da Abuja. Ya kan sa a kama mutane ya bar su cikin azaba, babu abinci har sai sun mutu.
Ya kara da cewa dan bindiga Baderu matashi ne ya na kuma cikin dabar da suke yawan kai hari da satar mutane a hanyar Abuja, hatta hare-haren da aka dinga kai wa a kwanakin baya a wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja, ya na daga cikin masu kitsa shi.
”Idan aka kashe Kacallah to fa an karya laggon wannan kungiya, an toshe barnar shigo da makamai ko kayan aikin da ‘yan fashin dajin ne daman ya ke samar da su. Karshe dole gayyar ta watse.