Babu Tausayi A Karin Kudin Lantarki A Yanzu – Atiku

IMG 20240316 WA0103

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi tir da yadda gwamnatin Najeriya ta ƙara kudin lantarki.

Babbanjagoran adawan kasar bai goyon bayan karin kudin shan wutar lantarkin da aka yi wa ‘yan rukunin farko da ake kira Band A. Atiku Abubakar ya soki karin kudin lantarki a Najeriya

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da kawo tsare-tsare masu zafi ba tare da ba da isasshen lokacin saukake wahalhalu ba.‘Dan takaran shugabancin kasar a zaben 2023 ya ce an yi karin kudin lantarkin ne a lokacin da ‘yan Najeriya suke tsakiyar kunci.

Wazirin Adamawa ya ce cire tsarin tallafin man fetur da karya darajar Naira da bankin CBN ya kawo karin wahala ga al’umma. “Kamfanoni za su fi tasirantuwa ta mummunar hanya. Bayan yawan ruwa da suke biya a kan bashin banki, suna kashe kudi sosai a kan dizil, da albashi mai yawa a dalilin sabon tsarin .”

“Mutanen shugaban kasa suna jefa tattalin arziki cikin matsala mai zurfi. Babu tausayin jama’a a manufofinsa.” “Yana da muhimmanci a fahimci tushen matsalar harkar wutar lantarki kafin a fito da wasu salon gyare-gyare.”

“Lokaci ya yi da za a duba saida kamfanonin lantarkin da aka yi da ya haifar da DISCOS.”  A bayanin da ya yi a shafin Facebook, Atiku ya ce dole a bi a hankali, a kawo tsare-tsaren da za su takaita wahalar da ake ciki. Sannan ‘dan siyasar ya ce sai NERC ta tashi tsaye, a inganta samun hasken wuta.

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply