Kaduna: Uba Sani Zai Kai Jihar Ga Tudun Mun Tsira – Yaro Mai Kyau

An shawarci jama’ar Jihar Kaduna da su sanya sabon Gwamnan jihar Sanata Uba Sani cikin adduo’i domin samun nasara wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.

Ɗan Majalisar dokokin jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi daga yankin ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu Honorabul Muhammad Auwal Yahaya wanda aka fi sani da Yaro Mai Kyau ya bukaci hakan a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

Ɗan Majalisar ya ƙara da cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin gogewa da zaɓaɓɓen gwamnan ya ke dashi ta fuskar cigaban ƙasa, wanda kowa ya ga haka a zaman da ya yi a majalisar Dattawa kuma babu shakka Jihar Kaduna za ta samu kyakkyawan cigaba ƙarƙashin jagorancin Uba Sani.

Honorabul Auwalu Mai Kyau ya taya zaɓaɓɓen gwamnan murnar shiga gidan Gwamnati, sannan ya yi addu’ar Allah ya shige mishi gaba wajen sauke nauyin jama’ar Jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply