NNPC Na Bin Najeriya Bashin Triliyan Biyu Da Biliyan 800 Na Tallafin Mai – Kyari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL na bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan biyu da biliyan 800 na tallafin man, a cewar shugaban kamfanin Mele Kyari.

Da yake magana a fadar shugaban ƙasa bayan kammala ganawa da Shugaba Bola Tinubu, Kyari ya ce sun yi maraba da jawabin shugaban na cewa tallafin mai ya ƙare.

“Dogayen layuka da aka fara yi a faɗin ƙasa ba abin mamaki ba ne, saboda ‘yan kasuwa na son su fahimci ma’anar maganar Tinubu cewa ‘tallafin mai ya ƙare’,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa biyan kuɗin tallafin, wanda NNPCL ke samarwa, ya hana kamfanin samun ribar da zai zuba a wasu harkokin kasuwancinsa.

Kamfanin man fetur, NNPC ya ce suna goyon bayan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi.

Shugaban kamfanin ya bayyana cewa suna da mai da zai wadaci ‘yan kasa har na tsawon wata daya.

Ya ce cire tallafin zai taimaka wa kamfanin ganin yadda a baya suke biyan kudi daga ribar kamfanin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply