Kaduna: An Yi Nasarar Damke Makasan Abdulkareem Na’Allah

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Rundunar ‘yan Sandan jihar ta yi nasarar kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da masaniya a kan kisan Abdulkareem Na’Allah, dan Sanata Bala Ibn Na’Allah mai shekaru 36.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, kwanaki kadan da suka gabata kenan da kama su. A ranar 29 ga watan Augustan 2021 aka tsinci gawar Abdulkareem, babban dan sanatan a dakin sa da ke Malali GRA a Kaduna.

Sai dai babu kwararan bayanai a kan wadanda aka kama amma dai shekarun su 20 da ‘yan kai da haihuwa ne.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kama mutanen ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Mohammed Jalige.

Labarai Makamanta

Leave a Reply