Gwamnatin Tinubu Ta Bar Jaki Ta Koma Dukan Taiki – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya soki karin kuɗin eutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi ya an mai cewa zai kara jefa ƴan Najeriya cikin tsanani ne da bakin talauci.

Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne gwamnati ta kara kuɗin wutar lantarki ga masu shanta a rana na aƙalla awa 20.

Sai dai tun bayan haka, da yawa mutane suka rika yin tir da wannan kari suna masu cewa yin haka zai daɗa jefa ƴan Najeriya ne cikin halin ƙakanikayi.

Shugaban ma mataimakin shugaban kasa ya ya tofa na shi albarkacin bakin inda ya ce karin za jefa ƴan Najeriya cikin wahalhalu da basu misaltuwa.

” Wannan gwamnati bata gama da matsalolin da ta jefa ƴan Najeriya ba tun bayan cire Tallafin da aka yi ba. Sai kuma ta bijiro da irin wannan kari, akwai rashin tausayi matuƙa a cikin haka.

Bayan haka, Atiku ya ce ba kawai mutane baamfanonin kasar nan dake amfani da wutar lantarkin duk za su ɗanɗana matsin da wannan karo zai janyo.

” Maimakon ƙarin da aka yi, abinda ya fi da cewa shine a san menene matsalar, sannan da yadda za a shawo kansa a gyara fanni, ba a rika ɗibga wa ƴan kasa ƙarin tsananin rayuwa da basu gama girgijewa daga na baya ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply