Ina Nan Daram A Jam’iyyar PDP – Wike

Rahoton dake shigo mana daga Fatakwal babban birnin Jihar Ribas na bayyana cewar Gwamnan jihar Nyesom Wike ya ce yana nan daram a PDP babu inda za shi, kuma zai cigaba da yaki don ganin an yi abin da ya dace.

Ya fadi hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar da wakilan mazabu 319 na jihar Rivers, a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal.

Ya ce babu gudu ba ja da baya, ba kamar yadda ake ta hasashe ba cewa zai iya barin jam’iyyar.

”Abin da na sha fada wa mutane shi ne idan ma akwai mai tunanin cewa za mu bar PDP to ya sake tunani. Za mu yi yakin da za mu yi ne a cikin jam’iyyarmu. Mu ba irin su ba ne da a 2014 suka fice daga dandalin Eagles Square. Sun manta. Sun fice suka je suka shiga APC. Ko ba haka ba ne?,” in ji Wike.

Jigo a jam’iyyar ya kuma yi bugun gaba cewa duk wanda ya gudu saboda rikici a jam’iyyarsa ba jarumi ba ne, kuma abin da ba zai taba yi ba kenan.

A kan haka ya shirya tattaunawa ta musamman da manema labarai gobe Asabar, inda zai fadi tantagaryar gaskiyar abin da ya sa yake yaki da wasu jiga-jigai a babban jam’iyyar adawar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply