Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Kuɗin Lantarki

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta sanar da karin kudin wutar lantarki na sama da kaso 50 cikin 100 na abin da kowane mai amfani da lantarki zai rinka biya a kasar.

Hukumar NERC mai kula da harkokin wutar lantarki ta ce matakin ya fara aiki daga farkon wannan shekara.

An ruwaito cewa sabon karin kudin ya shafi kowa da kowa sabanin wanda Gwamnati ta yi a watan Nuwamba da aka ce bai shafi marasa karfi ba.

Jama’ar Najeriya dai na cigaba da tattauna wannan mataki da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari ta ɗauka, inda akasarin ‘yan Najeriya ke nuna adawa da inkarin matakin gwamnatin, abin da suka kira da wani shiri na musguna wa jama’a kawai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply