Amfani Da Tsoffin Kudi Ya Haramta A Najeriya – Babban Banki

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu ruwan sa da umarni ko hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a makon da ya gabata, ko wanda za ta yanke a ranar 15 Ga Fabrairu.

Ya ce duk wani mai riƙe da tsoffin kuɗin Naira 200, 500 da kuma 1000, to ba shi da bambanci da mai kayan ƙarangar takardar tsire, domin ba zai iya hada-hada da kuɗin a yanzu ba.

Ya faɗi haka ne a ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara Ma’aikatar Harkokin Waje, a Abuja.

A ranar 8 Ga Fabrairu Kotun Ƙoli ta ƙara kwana bakwai daga wa’adin 10 Ga Fabrairu wanda Emefiele ya ƙara lokacin da ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Daura.

Sai dai kuma tun bayan da Kotun Ƙoli ta yi ƙarin wa’adin, CBN ba ta yi magana ba, sai yau, jajibirin ranar ƙarewar wa’adin, kafin a ji abin da Kotun Ƙoli za ta zartas kuma ranar Laraba, 15 Ga Fabrairu.

A ranar Litinin dai mafi yawan masu manya da ƙananan kasuwanci sun daina karɓar tsoffin kuɗaɗe. Amma lamarin ya fi muni a ranar Talata.

A ranar Talata ɗin ce kuma Emefiele ya bayyana cewa CBN ba zai ƙara ko kwana ɗaya daga tsohon wa’adin da ya bayar ba.

“To ai yanzu lamarin ya yi sauƙi sosai, tunda bankuna sun fara biyan mutane kuɗaɗe a kan kanta. Kuma masu POS su ma su na biyan kuɗaɗen.” Inji Emefiele.

“Saboda haka babu buƙatar a ƙara ko da wa’adin rana ɗaya kuma daga 10 ga Fabrairu.”

Emefiele ya zargi wasu ‘yan siyasa da laifin ɓoye sabbin kuɗaɗe.

“Wasu shugabannin mu su na sayen sabbin kuɗaɗe su na ɓoyewa, su na kimshewa saboda wasu dalilai. Ba na son bayyana abin da za su yi da kuɗin.” Inji Emefiele

Labarai Makamanta

Leave a Reply